Babu Wani Dalili Da Dai Sanya Ɗan Majalisar Tarayya Ya Samu Albashi Fiye Da Na Alƙali – Osinbajo

Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo a ranar Talata yace irin yanayin da Ma’aikatan Shari’a suke ciki, ya kamata ya zamanto yana janyo ra’ayin mutane zuwa ga ɓangaren.

Ƙwararren Lauyan wanda ya bayyana cewar Albashi da jindaɗin su, shine abinda zai sanya a samu nasara a ɓangaren, yace babu wani dalili da zai sanya Joji sun karɓi Albashi ƙasa da Ƴan Majalisar Tarayya.

Osinbajo ya bayyana haka a wani taron Ɓangaren Shari’a.
Mataimakin shugaban Ƙasar a jawabin da ya fitar ta hannun mai magana da yawun sa, Laolu Akande, ya bayyana wasu mahimman ɓangarori da zasu sanya a samu nasara a ɓangaren.

Yace ɓangarorin sune zaɓar kwararru a bangaren, da ƙarin girma, kasafin Kuɗi, da zubo da kuɗaɗe, gami da kyakkyawan albashi da jindaɗi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram