Sakataren gwamnatin jahar Katsina Mustapha Muhammed Inuwa ya ce babu sana’ar da ta kai ta sayar da abinci muhummanci da daraja ga al’umma.
Mustapha Inuwa ya bayyana haka ne a yayin da kungiyar masu sayar da abinci suka kai ma shi ziyara a ranar Talatar nan a Ofishinsa da ke sakatariyar jahar.
Inuwa ya ce sana’ar sayar da abinci ta shafi abubuwa da mutane da yawa musammamn idan aka lura da cewa dole ne kowa ya ci abinci mutum ko dabba babba da yaro namiji ko mace
Ya ce in aka lura da irin rawar da sana’ar ta ke takawa wajen fadada tattalin arziki, kamar yadda ta shafi masu sana’a cefane da da masu markade da icce da gas na girki da duk sauran wani abu da ya zama dole sai da shi abinci zai tabbata.
Hakazalika sakataren gwamnatin ya ba su tabbacin cewa gwamnati zata yi duk mai yiwuwa domin ganin ta bada gudunmuwarta wajen sayen abinci daga gare su a yayin gudanar da wasu taruka na ta.
Daga karshe ya shawarce su da su rinka tsafftace abincinsu
Tun da farko a yayin jawabinsa, Shugaban kungiyar, Aminu Kabir, ya ce sun zo ne a kungiyance domin gabatar da kansu sannan ya gabatar da kokon bararsu na bukatar a rika sanyo su cikin al’amuran da suka shafi sana’arsu.