Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje yace bazai ɓata lokaci wajen zartar da hukuncin kisa ga Abdulmalik Tanko, idan har aka kawo a gaban shi.
Tanko wanda shine mai Mallakin Makarantar Noble Kids Academy dake Ƙaramar Hukumar Nasarawa ta Kano, ya tabbatar dacewa ya kashe ƴar shekara Hanifa Abubakar, ɗalibar daya sace a watan Disamba na shekarar data wuce.
A ranar Litinin, Gwamnan yasha alwashin biyayya ga doka na sanya hannu domin zartar da hukuncin kisa ga Tanko, idan har Kotu da zartar da hukunci.
Ya bayyana haka a lokacin da yakai ta’aziyya da mataimakin sa Dr Nasuru Yusuf Gawuna, da Shugaban Masu Rinjaye, da sauran wasu manyan jiga-jigan Gwamnati a gidan iyalan dake Dakata/Kawaji.
“Muna da tabbatar maku dacewa, Kotu zata yi adalci akan ta. Babu abinda zamu ƙyale, duk wanda aka samu yana aikata mummunan laifi, ba tare da ɓata lokaci zamu zartar masa da Hukunci. A matsayin mu na Gwamnati, tuni mun fara hakan.
“Kundin tsarin mulki ya ce idan har aka zartar da hukunci, to Gwamna ne zai zartar da’ita. Ina baku tabbacin cewa bazan ɓata daƙiƙa guda wajen sanya hannu.
Yace Gwamnati zata ɗauki nauyin iyalan Hanifa da aka ɗauki ran ta.
Uwargidan shugaban Ƙasa Aisha Buhari tayi kira ga Tanko daya tabbatar ya zartar da hukunci a bainar jama’a.