A kalla mutane tara ne suka mutu yayin da wasu 10 suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kauyen Sabaru kusa da garin Gamoji a karamar hukumar Gaya a jihar Kano.
Hadarin da safiyar yau ya hada da Toyota Hiace Bus da wata mota kirar Sharon da ta taho daga wata hanya.
Wani ganau ya shaida wa Daily Trust cewa motar bas ta taho ne daga garin Azare na jihar Bauchi zuwa Kano, yayin da motar ta taso daga Kano zuwa Dutse suka yi karo a kauyen.
An kai gawarwakin wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Gaya inda ake kokarin jin ta bakin ‘yan uwansu, yayin da wadanda suka jikkata ke karbar kulawa a asibitin
Kakakin hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Jigawa, Ibrahim Gambo ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce hatsarin ya rutsa da wata motar bas Toyota Hummer, mai lamba DRZ, 846, XA da kuma motar Sharon mai lamba DAL, 830, XA.
Gambo ya ce daya daga cikin motocin da ke gudun wuce kima ya rasa yadda zai yi bayan ya tsallake rijiya da baya, lamarin da ya yi sanadin yin karon taho mu gama
Jami’in ya ce mutane 19 ne suka yi hatsarin, wanda ya hadar da maza 17, mata biyu wadanda ke cikin dukkannin motocin biyu.
Jami’in ya kara da cewa dukkan wadanda suka mutu maza ne, yayin da mata biyu na daga cikin wadanda suka samu munanan raunuka