Wata Gobara Ta Tashi Ta ƙone gawa sama da 400

Ɗaruruwan gawarwaki sun ƙone a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya bayan da wata gobara da ta tashi ta dauki tsawon sa’o’i tana ci a sashin ajiye gawa na babban asibitin garin Onitsha na jihar.

Wasu shaidu da suka gane ma idanuwansu lamarin sun fada ma manema labarai cewa, gobarar ta fara tashi ne daga bayan dakin ajiye gawarwakin.

BBC ta ambato cewa, a yanzu haka hukumomi a jihar na ci gaba da gudanar da bincike domin tantance da gano musabbabin tashin gobarar.

A ɓangaren iyalan mamatan da gawarwakinsu suka ƙone kuwa, sun shiga halin ruɗani inda suka je asibitin suna ta kuka don ba a ko iya gane gawarwakin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram