Yadda Wasu Da Ake Zargin Ƴan Ƙungiyar Asiri Ne Suka Fafata Har Aka Rasa Rayuka A Jihar Benue

An kashe mutane uku a wata arangama da ake zargin na ‘yan kungiyar asiri ne a unguwar Corner Stone kusa da Gyado Villa a cikin Garin Makurdi babban birnin jihar Benue.

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:40 na yammacin ranar Lahadi bayan da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka tsunduma kansu cikin wani fadan bindiga a yankin da lamarin ya shafa.

Wani ganau ya shaida wa wakilin Majiyar Jaridar Jakadiya a ranar Litinin cewa biyu daga cikin ukun da suka mutu ‘yan uwan ne, Kuma ​​iyayensu daya ne.

Shaidan ya ce, karar harbe-harbe da kururuwar wadanda abin ya rutsa da su na iya firgita Mutum, inda nan take aka harbe mutane uku.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO), SP. Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce mutane biyu ne suka mutu yayin da daya ke kwance a asibiti.

“An tabbatar da faruwar lamarin. Ana ci gaba da bincike. Biyu sun mutu yayin da daya ke kwance a asibiti,” in ji Anene.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram