COVID-19: Za A Kaddamar Da Rigakafin Kananan Yara A Najeriya

A kokarin ta na yaki da cututtukan kananan yara da manya a Najeriya, hukumar kiwon lafiya matakin farko ta kasar, NPHCDA, ta kaddamar da rigakafin kananan yara da sauran ayyukanta a wuraren da ake rigakafin cutar Korona.

Da yake yi wa ‘yan jaridu jawabi a Abuja a ranar Talata, shugaban hukumar NPHCDA din na kasa, Dr. Faisal Shu’aibu, ya bukaci iyaye da ke da jarirai tun daga haihuwa har zuwa watanni 23 da su kai su cibiyoyin rigakafin cutar Korona domin yin rigakafin sauran cututtuka.

Dr. Shu’aibu ya ce, manufar ita ce a tabbatar da ganin cewa, a yayin da ake kokarin shawo kan cutar Korona, ba a manta da sauran hakkokin da ke wuyan hukumar ba, ciki har da hana barkewar cututtukan yara da ke da hanyoyin kariya.

Ya ce idan aka lura, za a ga cewa, yawan masu kamuwa da cutar Korona ya karu a lokacin da bukukuwan hutu suka karato ba wai a Najeriya kadai ba, har ma da duniya baki daya.

A Najeriya, mutane da dama da ba a yi wa rigakafin cutar ba sun yi ta karakaina daga birane zuwa kauyuka, sannan daga kauyuka zuwa birane.

Haka nan kuma, an ga yadda aka samu bullar sabbin nau’o’in cutar irin su IHU a kasar Faransa da Deltacron a Cyprus da kuma Omicron wadda ke yaduwa cikin hanzari.

Shu’aibu ya kara da cewa, ana samun karuwar ‘yan Najeriya da ke kamuwa da cutar Covid-19 din, sai dai dacen da aka yi, cutar ba ta yin tasiri sosai a tsakanin wadanda suka rigaya suka karbi rigakafin.

A cewar sa, rigakafin na kare mutum daga tsanantar cutar da kwanciyar asibiti da kuma rasa rai.

Shugaban hukumar na mai sanar da al’umma cewa, a wannan mataki na gangamin yi wa dimbin jama’a rigakafin Koronar, an tsara saka shi cikin shirin rigakafin sauran cututtukan kananan yara da ma sauran aikace-aikacen hukumar.

Dr. Shu’aibu ya ce, ya zuwa ranar Talata, 25 ga watan Janairu, sama da mutum miliyan 14 sun karbi rigakafin farko na Covid-19, a yayin da sama da miliya 5 da rabi na ‘yan Najeriya suka kammala rigakafin.

Ya bayyan cewa, jihohin Nasarawa da Jigawa da Ogun da Kwara da kuma Abuja, su ne suka fi yawan mutanen da suka karbi rigakafin cutar ta Covid-19 a kasar baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram