Ina Fatan Jam’iyyar APC Ta Ƙara Amshe Mulkin Najeriya A 2023 – Garba Shehu

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kain jama’a Malam Garba Shehu, ya bayyana fatansa na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mikawa wata gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki ne Mulki a shekarar 2023 Mai zuwa.

Ya yi wannan jawabi ne a takaice bayan kammala taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC) daya gudana a yau Laraba a Abuja, inda da yake mayar da martani kan wata tambaya da ke nuna cewa Shugaban kasa ya ingiza matsalar cire tallafin man fetur ga gwamnati mai zuwa tare da shirin ba da shawarar tsawaita wa’adin watanni 18 ga Majalisar Tarayya. don aiwatar da Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA) da aka shirya farawa a farkon watan Fabrairu Mai zuwa.

Mai taimaka wa shugaban kasan, wanda ya nuna cewa kamar an riga an kafa gwamnati mai zuwa, ya mayar da martanin cewa, : “Amma ita (Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsare ta Kasa, Hajiya Zainab Ahmed) ta amsa muku. Na farko abin da wannan ke nuna maka shi ne Shugaban kasa ya amsa kuma za mu mika wa gwamnatin APC Mai zuwa, in Allah Ya yarda.”

Ya Kuma kara da cewa, “Ministar kudin, wacce da farko ta mayar da martani kan tambayar, ta ce, “Na san Mai Girma Shugaban shine zai ci gaba da kasancewa Shugaban Najeriya har zuwa watan Disamba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram