Da ɗuminsa: Jirgin Saman Yan sanda Ya Yi Hatsari A Jihar Bauchi

Da ɗuminsa: Jirgin Saman Yan sanda Ya yi Hatsari a Jihar Bauchi

Wani jirgin sama mai saukar ungulu na ‘yan sanda da ya taso daga Abuja ya yi hatsari a filin tashi da saukar jiragen sama na Bauchi, kamar yadda Hukumar Binciken Hatsarin jiragen Sama ta kasa ta ta bayyana a ranar Alhamis.

Koyaya, ba a sami asarar rai ba, in ji hukumar ta AIB.

A Cikin wata Sanarwar da ta fitar ta ce,“A ranar 26 ga Janairu, 2022, Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (NAMA) ta sanar da Ofishin Binciken Hatsarin cewa, An Sami wani hatsarin da ya rutsa da wani jirgin sama mai lamba kira Bell 429 mai lamba 5N-MDA, kuma mallakin rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF),” inji sanarwar. yace.

“Hatsarin ya faru ne a ranar 26 ga watan Janairu, 2022 da misalin karfe 7:30 na yamma Agogon Najeriya, a filin jirgin Saman Bauchi.

“Jirgin rundunar ya taso ne da misalin karfe 16:54 UTC zuwa Bauchi tare da mutane shida dauke da 5,500ft.

“Akwai wasu raunuka amma babu Mutuwa” kamar yadda Hukumar ta bayyana.

Hukumar ta Kuma ce ta na bukatar agajin jama’a da wasu bayanai da zasu taimaka mata wajan samun duk wani faifan bidiyo, shaidan musabbabin faruwar lamarin, domin gudanar da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram