Yan bindiga Sun Sace Ɗan uwan ​Jonathan

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dan uwan ​​tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan Jephthah Robert a gidansa da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

An gano cewa har yanzu wadanda suka yi garkuwa da su ba su tuntubi danginsa ba tun bayan sace shi a ranar Litinin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da yin garkuwar, ya ce suna ci gaba da kokarin kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi tare da kamo wadanda suka sace shi

Duk da cewa haryanzu Babu cuiakakkun bayanai kan yadda akayi Garkuwa da shi amma ana samun karuwar satar mutane a jihar Bayelsa a baya-bayan nan.

A ranar Litinin din da ta gabata ne kwamishinan ciniki da saka hannun jari na jihar, Federal Otokito, ya samu ‘yanci bayan ya shafe kwanaki biyar a gidan masu garkuwa da mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram