Dalilan Da Suka Sanya Muka Kama Tsohon Kwamishinan Kano, Magaji — Ƴan Sanda

Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kano ta sanar da dalilan da suka sanya suka kama tsohon Kwamishinan Ayyuka Mu’azu Magaji.

Magaji, wanda ya kasance yana caccakar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ƴan sanda sun kama shi a Abuja, jim kaɗan bayan ya tattauna da gidan Talabijin na Trust TV a Utako a Daren Alhamis.

Tuni dai aka kaishi Kano, kuma yayi kwana ɗaya a hedikwatar ƴan sanda dake Bompai.

Dayake jawabi da Jaridar Daily Nigerian, a ranar Juma’a, Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar SP Abdullahi Haruna, ya bayyana cewar ƴan sanda sun kama shi ne bayan Magaji yaƙi amsar gayyatar da suka yi mashi domin yi masa tambayoyi duk da gayyatar shi da akayi da dama.

Haruna ya bayyana cewar ƴan sanda sun gayyaci Magaji biyo bayan umarnin da Kotu ta bayar na a bincike shi.

Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan yace ” ana bincikar sa akan cin mutunci, da ɓata suna, da zagi, sa yaɗa bayanan ƙarya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram