Wani dalibin shekarar karshe a Sashen Laburare da Kimiyyar yada Labarai na Jami’ar Bayero Kano (BUK), ya rasu.
Dalibin, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun jami’ar, Lamara Garba,ya fitar yace dalibin mai suna Babangida Ahmed ya rasu ne da sanyin safiyar Juma’a, a dakin kwanan dalibai na makarantar.
Sanarwar ta kara da cewa marigayi Ahmed ya fadi ne a dakin kwanan sa a lokacin da yake shirin zuwa masallaci domin yin sallar asuba.
Majiyar Jarida Jakadiya ta rawaito cewa Marigayin ya fito ne daga karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi.
“Tuni Hukumar Jami’ar ta tuntubi iyayensa game da lamarin kuma za a kai shi garinsu domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,” in ji sanarwar a wani bangare.
“A cewar daya daga cikin abokan aikin marigayin Babangida ya fita daga dakin da misalin karfe 4:30 na safe, inda nan take ya yi kasa a gwiwa ba tare da wata alamar rai ba, kafin a garzaya zuwa asibitin jami’ar da ke harabar jami’ar.
”An ce an kawo gawarsa (BID) dake asibitin Jami’ar.
“Kafin rasuwarsa, marigayin ya ziyarci Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) inda ya rika ganin likita kan wata cuta da ba a bayyana ba.
Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas, a madadin hukumar jami’ar ya jajantawa ‘yan uwa da abokan arziki na marigayin tare da addu’ar Allah ya jikansa da rahma yasa aljannace makomar sa.