Ba Rashin Lafiya Ta Kai Tinubu Landan Ba, Ya Je Ne Domin Neman Shawarwari — Cewar Mai Taimaka Masa

Jigon Jam’iyyar APC na Ƙasa Bola Tinubu yana nan lafiya ƙalau, inji Ma Magana da Yawun sa Tunde Rahman.

Rahman ya tabbatar da cewa ɗan shekara 69, tsohon Gwamnan Lagos ya tafi ƙasar waje domin gudanar da wasu tarurruka, da kuma cigaba da neman shawara akan aniyar sa ta tsayawa takarar Shugaban Ƙasa a shekarar 2023.

Mai Magana da Yawun a saƙon karta kwana da Jaridar PUNCH ta aika masa a ranar Juma’a, yace jigon Jam’iyyar APC zai dawo Najeriya sati mai zuwa.

Yace “zuwan Asiwaju Ƙasar Landan baya je bane domin hutu, ko kuma domin bashi da lafiya.

“Yana a ƙasar wajen, amma yana gudanar da taro da kuma tattaunawa akan siyasa.

“Ko yana gida ko yana ƙasar waje, aikace-aikacensa suna da yawa. Da yawan mutane bazasu iya irin abubuwan da yake ba. Wannan ya nuna irin kaifin basirarsa da kuma ƙarfin sa, da jajircewa domin samar da cigaba,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram