Dara Taci Gida: Yan Sanda Sun Kama Soja A Jihar Yobe, Bisa Zargin Fashi Da Makami

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta ce ta kama wasu mutane uku da suka hada da soja guda da laifin hada baki, fasa gidaje da kuma fashi da makami.

An ce wadanda ake zargin sun kai farmaki gidan wata Hajiya Aisha Usman da ke unguwar Sabon-Pegi a Damaturu da tsakar dare.

An dai ce wadanda ake zargin dauke da muggan makamai da suka hada da bindiga kirar AK 47, sun yi awon gaba da kudi naira 250,000, da mota kirar Peugeot saloon 307 da kuma wayar Nokia na wanda lamarin ya rutsa da su..

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar, ya ce wadanda ake zargin sun yi wa matar da danta, Ahmed Umar mai shekaru 17 raunuka, bayan daure su da su kayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram