Kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta dakatar da kasar Burkina Faso daga zama mamba.
Dakatarwar na zuwa ne bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar wanda ya sanya ta zamo kasa ta 3 da kungiyar za ta hukunta bisa irin wannan dalili a cikin watanni 18.
ECOWAS din ta bayar da wannan sanarwar ce kwanaki bayan sojoji masu tayar da kayar baya sun tilasta wa zababben shugaban kasar, Marc Kabore, sauka daga kan mukamin sa.
Sojojin sun tafi gidan talabijin na kasar inda suka bayar da sanarwar karbe mulkin kasar wadda suka ce matsalar tsaro ta mamaye ta.
Masu juyin mulkin sun bayyana cewa, shugaba Kabore ya gaza shawo kan matsalar tsaron da ta lakume dubban rayukan ‘yan kasar a lokacin mulkin sa.
A ranar Alhamis ce shugabannin kasashen Afirka ta Yamman suka tattauna ta yanar gizo a kan batun juyin mulkin na Burkina Faso, kuma ana sa ran tura wata tawaga zuwa babban birnin kasar, Ouagadougou, nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS mai ci, ya kira yaduwar juyin mulki a Afirka ta Yamma da cewa, wani yunkuri ne na rusa tsarin dimokuradiyya a yankin kuma sauran sassan duniya na sanya idanu domin ganin yadda za a kawo karshen hakan.
Ana sa ran manyan hafsoshin tsaron kasashen ECOWAS din su tashi zuwa kasar ta Burkina Faso a ranar Juma’a kafin tawagar ministocin yankin su je kasar ranar Litinin.
A lokacin taron na kusan awa uku, shugabannin kasashen na ECOWAS sun kuma yi kiran da a saki shugaba Kabore da sauran mukarraban sa da ke daure.