2023: APC Ta Gama Tasiri Tunda Ta Ɓata Rawarta Da Tsalle – Sanata Tofowomo

Sanata mai wakiltar mazabar Ondo ta kudu a majalisar dattawa, Nicholas Tofowomo, ya sha alwashin barin siyasa maimakon ya koma jam’iyyar APC Mai mulki.

Tofowomo, sanata ne mai ci a jam’iyyar PDP, wanda ya bayyana APC a matsayin matacciyar jam’iyya, ya ce jam’iyyar da ke mulki ba za ta iya siyan ‘yan Najeriya a 2023 ba.

Sanatan ya bayyana haka ne a karshen makon Nan a wani taron da ya shirya wa matasa a yankin kudancin jihar inda aka horas da su kan fasahar ICT.

“Maimakon in koma APC, zan bar siyasa saboda APC matacciyar jam’iyya ce a Najeriya. Sun durkusar da tattalin arzikin kasar nan. Ni dan PDP ne safe da rana da kuma dare. Kuma idan na bar PDP, zan koma gida.

“Idan ka dubi APC, ta lalata tattalin arzikin Najeriya, sun samu komai a yanayi Mai kyau, A lokacin da suka karbi mulki buhun shinkafa naira 6,000, yanzu ya kai kusan N35,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram