Ousmane Dembele yana tattaunawa kan komawa Paris Saint-Germain na dindindin.
Barcelona na son fam miliyan 20 domin siyan dan wasan bayan ta gaya wa Dembele wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana ya nemi wata kungiya.
Dembele ya cimma yarjejeniya ta baka-da baka tsakanin shi da PSG ranar Lahadi, duk da sha’awar da kungiyoyin Premier League ke masa, in ji Skyspors.
Wakilansa Moussa Sissoko da Marco Lichtsteiner suna aiki don nemo mafita ga dan wasan gefen.
Barcelona ta sake gaya wa Dembele ranar Alhamis cewa ya nemi wata kungiyar, idan ba ya son ya rattaba hannu kan tayin da suka yi masa a baya na sabon kwantaragi tare da rage albashi.
Dembele ya gwammace ya ci gaba da zama a Barcelona na sauran kwantiraginsa da ya rage a yanzu amma Barcelona ta bayyana cewa tana son ya fice a yanzu kuma har ma ta yi barazanar barin shi batare da buga wasanni ba, idan ya zauna.
Dan wasan mai shekaru 24, ya koma kungiyar ne daga Borussia Dortmund kan kudi fam miliyan 135 a bazarar 2017 – ‘yan makonni bayan da Neymar ya koma Paris Saint-Germain a kudi Mafi yawa a tarihin site da sayarwar Yan wasan kwallon kafa na duniya – amma ya yi fama da rauni a tsawon lokacinsa a Spain.
Dembele ya fara buga wasanni shida kacal a kakar wasa ta bana inda ya ci kwallo daya tilo a gasar Copa del Rey da suka doke Linares a farkon wannan watan.