Mai shekaru 61 Fasto Tracey Sydnor ana zargin cewa ɗan ta Mai suna Kenji Francis ya caccaka mata wuƙa har sau 15 a gidan ta dake Wyona a New York ta Amurka.
Mamaciyar wadda itace Fasto a cocin Upper Room Baptist dake Rockaway a Bedford-Stuyvesant an kashe ta a ranar Asabar 29 ga watan Janairu.
Acewar Jaridar Daily News abokin Sydnor Terrence Reed tace “mutumce data haɗa komai, babu wani abun rashin jindaɗi da zaka faɗa akan ya.”
Ƴan sanda sunce ya Caccaka mata wuƙa a ƙalla sau 15 har da wuyan ta, kunne da hannaye.
Motar daukar marasa lafiya tayi saurin kai ta Asibitin Brookdale Amma bata rayu ba.
Ɗan Sydnor mai shekaru 40 Francis tuni aka kama shi akan zargin aikata laifin.