Sananniyar mai Safarar Mata zuwa Kasar waje Joy Shandy Okah, Jami’an Hukumar Hana Safarar Bil’adama ta Najeriya sun kama ta haɗin gwiwa da Ƴan Sandan New Delhi a wani samame da suka yi.
Samun nasarar kama ta da akayi, ya sanya an ceto mata guda 4 da aka tilasta wa Karuwanci (an ɓoye sunan su) a New Delhi, India.
Shugaban Hulɗa da Jama’a na Hukumar Stella Nezan Wanda ya bayyana haka a ranar 31 ga watan Janairu, ya bayyana cewar Darkta-Janar Dr Fatima Waziri-Azi a shigar ta ofis tasha alwashin kamo fitattun masu safarar bil’adama a faɗin duniya, tare da gurfanar dasu a gaban ƙuliya gami da kwace dukiyar da suka samu tare da baiwa wadanda suka yi safarar su.
Dayake bayyana yanda aka samu nasarar kama ta, Shugaban Yaɗa Labaru na NAPTIP Mrs Angela Agbayekhai, yace umarni da goyon baya daga Darkta-Janar shiya bada nasarar cimma nasarar.
“NAPTIP ta hada kai da wata NGO a Vihaam-WMS ta hanyar bayanan sirri, wanda ya haddasa samun nasarar kama mai safarar mutane a New Krishna dake New Delhi, India.