Mutane Da Yawa Sun Mutu A Guinea-Bissau Bayan Yunkurin Juyin Mulki, In ji Shugaban Kasar

An yi wunkurin juyin mulki a kasar Guinea-Bissau da ke yammacin Afirka inda mutane da Dama suka Mutu.

Shugaban kasar Umaro Cissoko Embaló ya ce an shawo kan juyin Mulkin da akayi yunkurin yi a kasar, yana mai cewa harin zagon Kasa ne ga mulkin dimokradiyyar da kasar ke more wa.

An yi harbe-harbe a kusa da ginin gwamnati kasar a yammacin jiya Talata a Bissau babban birnin kasar inda aka ce shugaban na gudanar da wani taron da majalisar ministocin kasar.

An ce sojoji sun tsare shugaban kasar da ministocinsa, yayij da aka Kai wani mummunan farmaki, lokacin da suke tsaka da gudanar da taron

Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai da ba a san ko su waye ba sun kai hari fadar gwamnati a lokacin da shugaba Embaló ke ganawa da firaminista Nuno Gomes Nabiam a cikin fadar, kamar yadda rahotanni daga kasar suka bayyana.

Wata majiyar tsaro da ba ta so a bayyana sunan ta ta shaida wa BBC cewa ‘yan bindiga sanye da kayan farar hula ne suka bude wuta tare da kashe dan sanda guda.

Shugabannin yankin Afirka ta Yamma sun bayyana lamarin a matsayin yunkurin juyin mulki inda suka bukaci sojojin da su koma barikin su.

Sai dai har yanzu ba a fayyace abin da ya faru ba: Har yanzu ba a san ko su wane ne suka jagoranci Kai wannan hari ba, kuma shugaban kasar bai bayar da takamaiman adadin wadanda aka kashe ba.

Kasar Guinea Bissau na daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, wacce kasar Portugal da ta yi wa mulkin mallaka, ta fuskanci juyin mulki tara ko yunkurin juyin mulki tun daga shekara ta 1980 zuwa yau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram