Ta’addanci Yayi Sanadiyar Mutuwar Ɗalibai 167, Malamai 3 A Jahar Yobe

Gwamnatin Jahar Yobe tace ta’addancin Boko Haram ya kashe rayuka 167 na ɗalibai, da malamai guda 3 a Jahar.

Haka zalika, wasu ƙarin ɗalibai 86 sunji munanan raunuka, biyo bayan harin da suka yi, a ƙoƙarin su na hana karatun zamani a Jahar.

Mataimakin Gwamnan Jahar kuma Shugaban Kwamitin Asusun tara kuɗaɗe Idi Barde Gubana ya bayyana haka ga Manema Labaru akan rahoton kwamitin na cigaba da aka samu.

Gubana yace matsalar ce ta sanya Gwamnatin ta sanya dokar gaggawa ga ilmi a Jahar.

Yace Gwamnati na ƙara inganta hanyoyin da za’a samu ilmin firamare dana Sakandire ta hanyar gina ƙarin Makarantu, musamman na mata da masu buƙata ta musamman.

A cewar Gwamnatin tana kuma maida hankali wajen ɗaukar ma’aikata, horas dasu, da kuma inganta jin daɗin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram