Shugaba Buhari Ya Taya Amaechi Murnar Samun Sarauta A Daura

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya murna ga wasu jiga-jigan APC Ministan Sufuri Kuma Darkta-Janar na Yaƙin neman zaɓen sa Rotimi Amaechi da kuma ɗan Kasuwa Nasiru Danu akan naɗa su sarauta da Masarautar Daura tayi a ranar Asabar.

Saƙon taya murna na Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Mai Taimaka masa akan Kafafen Yaɗa Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a, yana mai cewa cigaba ta fuskar layukan dogo abun a yaba ne.

Buhari ya bayyana naɗa Amaechi a matsayin Ɗan Amanar Daura a matsayin wata manuniya na jajircewar sa, da kuma kyakkyawan fahimta dake tsakanin kabilu.

An naɗa Danu a matsayin Tafida Babba.

Ya yabawa Ministan “ga irin yadda yake aiki da ƙarfin sa domin kawo canji da aka yiwa ƴan Najeriya alƙawari ya zama gaskiya. Kuma canjin da ake gani a ɓangaren sufuri a matsayin abun a yaba.”

Duk da Shugaban Ƙasa bazai halarci wurin ba, ya naɗa wata tawaga data ƙunshi Ministan Albarkatun Ruwa Sulaiman Adamu, da Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika, gami da Babban Mai Taimaka masa akan Kafafen Yaɗa Garba Shehu su wakilce shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram