A dalilin damuwa da matsalar tsaro dake ta yawaita a Ƙaramar Hukumar Toro ta Jahar Bauchi, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed a ranar Asabar, yayi kira ga Shuwagabannin Ƙaramar Hukumar da Masu rike da Sarautun gargajiya dasu zama masu haƙuri akan baƙi dake zuwa a yankunan su daga maƙwabtan Jahohi.
Gwamna Mohammed ya bayyana haka a lokacin da yake ƙaddamar da shirin bada tallafi na Gwamnatin sa a yankin.
Gwamnan ya bayyana damuwa na yadda Ƙaramar Hukumar Toro ke fuskantar matsalolin tsaro, yana mai ƙara dacewa wannan ba yana nufin mazauna yankin ƴan ta’adda bane, sai dai saboda yankin da suke yana maƙwabtaka da iyakokin Yankin Arewa Maso Yamma, da Arewa ta Tsakiya, gami da yankin Arewa maso Gabas na Ƙasar.
Ya bayyana cewar yanayin inda suke zaune shine ya haddasa masu matsalar tsaro.
A cewar sa, hadakar jami’an tsaro a Jahar, ana tura su yankin, yana mai bayyana damuwa cewa Karamar Hukumar ita kaɗai ce a Jahar dake fama da matsalar.
Yace Gwamnatin sa na bakin ƙoƙarin domin magance matsalar, kuma zata cigaba da yin haka.
“Ina kira ga Al’ummar Toro su san cewa matsalar tsaro ta Al’umma ce. Muna da Haɗakar Jami’an tsaro da ake turowa a Toro.
Ya ƙara dacewa Dajin Lame da yafi Kowane a Najeriya, shima yana ɗaya daga cikin dalilan da suka sanya suke zuwa su zauna a wurin, yana mai cewa duk da an baiwa mutane dama su zauna amma ƴan ta’adda ba’a bukatar su a Jahar baki ɗaya.