Ko Za A Bani Billion Ta Dollar Don In Bada Sarauta Wallahi Ba Zan Ba Mutum Ba Duk Kuɗinshi ko shine Ɗangote – In Ji Sarkin Daura

Mai martaba Sarkin Daura Umar Faruq Umar ya bayyana cewa, ba yana bada sarauta ba ne don kwaɗayi.

Sarkin ya faɗi haka ne jim kaɗan bayan kammala naɗin sarautar da yayi ma Ministan Sifuri na Najeriya Chibuike Rotimi Amaechi a matsayin Ɗan-Amanar Daura da Alhaji Nasiru Haladu Danu a matsayin Tafida-babba a jiya Assabar a fadarsa da ke garin Daura a jahar Katsina.

Alhaji Faruq Umar ya ce shi yana bada sarauta ne don cancantar mutum kawai.

Yana mai cewa irin ayyukan alkhairan da Ministan yayi ma garin Daura shi ne ya sanya ya bashi wannan sarauta ta Ɗan-amanar Hausa.

Ya ce halin ƙauna da Amaechi ya nuna ga Daurawa abin a saka mashi ne da sarauta mai girma irin wannan.

Sarkin ya ƙara jaddada cewa ba zai bada sarauta ga kowa ba don kwaɗayin kuɗi ko don tsoro ko da kuwa za a bashi bilyon na dola ba zai yi ba.

Mu ba mu bada sarauta don kuɗi duk kuɗin mutum, ko shi ne Ɗangote.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram