Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutum 7 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna

Jami’an tsaro sun kubutar da wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su daga hannun ‘yan bindiga da suka kai farmaki Ungwan Garama, da ke yankin Maraban Rido na karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

An ruwaito cewa an samu kiran gaggawa daga al’umar yankin inda jami’an tsaro suka yi gaggawar kai daukin.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da kula da Harkokin cikin gida na jihar Kaduna ne ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce karfin wutar da sojojin suka yi ya tilasta wa masu Garkuwan gudu.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi amfani da toshe hanyar tserewar ‘yan fashin, inda kuma suka samu nasarar kubutar da mutane bakwai da aka yi garkuwa da su.

Aruwan ya ce dukkanin wadanda aka ceto sun koma ga iyalansu, inda ya ce Gwamna Nasir El-Rufa’i ya yabawa jami’an tsaro bisa irin namijin kokarin da suka yi da kuma saurin daukar matakan da suka dace.

Gwamnan ya mika gaisuwarsa da fatan alheri ga wadanda aka ceto daga miyagun

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram