2023: Ƴan Najeriya Na Fama Da Rashin Ƙwararrun Shuwagabanni Masu Hangen Nesa – IBB

Tsohon Shugaban Mulkin Soji a Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayi nuni dacewar a halin yanzu suna fama da rashin Shuwagabanni ƙwararru, jajirtattu, masu hangen nesa kuma masu inganta ƙabilanci a faɗin Ƙasar.

Babangida ya bayyana haka a lokacin da Shugaban Jam’iyyar PDP Sanata Iyorchia Ayu tare da mambobin gudanarwa suka kai masa ziyara a gidan shi dake Hilltop Mansion a Minna, Jahar Niger.

Tsohon shugaban Mulkin Sojin wanda ya karanta jawaban da aka tsara, ya bayyana buƙatar dake akwai ga Shuwagabanni dasu ƙara himma su kula da yanayin yadda jam’iyyu suke a ƙasar, domin bin abinda mutane suke so.

Tunda Farko, Sanata Ayu ya bayyana cewar yazo ne da mambobin gudanarwa na Jam’iyyar domin ziyartar Shugaban gami da neman albarkar shi, da samun wani abu daga ilmi a matsayin na uba ga Jam’iyyar PDP.

Yace ziyarar ta zama dole musamman a yanzu da ƙasar ke fama da matsalolin tsaro da rarrabuwar kawuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram