Gwamnati Ba Ta Damu Ba, Kuma Ba Ta Son Cigaban Ilimi – Inji ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa tace Gwamnatin Najeriya bata son Cigaban ilmi a Ƙasar.

Dayake jawabi bayan ya kammala gangami da taron ƙungiyar a Jami’ar Lagos, wadda akayi amfani da’ita domin kammala gangamin wayar da kan mutane akan al’amuran ASUU, Jami’in Shiyyar na ASUU Dr Adelaja Odukoya yace sun gaji da Alƙawurran Gwamnati ba tare da cikawa. Ya ƙara dacewa Gwamnati bata maida hankali akan abubuwan da suke so ba.

Malaman sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya data sanya hannu tare da ƙaddamar da Alƙawarin data ɗauka tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya wanda ake saran a riƙa yin dubi dashi duk bayan shekaru uku.

Yace “wayar da kan yana da matuƙar ilmantar da al’umma akan ƙin girmama yarjejeniya data shiga da ƙungiyar a watan Disamba na shekarar 2020 kafin ta dakatar da yajin aikin ta.”

Yankin ASUU na Lagos ya ƙunshi: Jami’ar Lagos, da Gwamnatin Tarayya ta Noma Abeokuta, da Jami’ar Olabisi Onabajo dake Ago-Iwoye da Jami’ar Lagos, da jami’ar ilmi ta Tai Solarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram