Ku Zargi Gwamnatin Tarayya Idan Muka Rufe Jami’o’i – Cewar ASUU

Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Fasaha dake Owerri, reshen Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ranar Laraba tace a kada a zargi Malamai idan harkokin karatu ya tsaya cak a Jami’o’i.

Ƙungiyar ta zargi Gwamnatin Tarayya ta lalata yanayin ilmi a ƙasa, tare da tauye makomar ɗaliban Najeriya.

Shugaban Ƙungiyar ASUU reshen Jami’ar Chinedu Ihejirika ya bayyana haka a taron Manema labaru a Owerri, inda yace Gwamnatin Tarayya tana ingiza ASUU domin ta kulle makarantu dole a faɗin Ƙasa, ta hanyar ƙin girmama Yarjejeniyar Fahimta da suka yi a shekarar 2009.

Malaman sunce yajin aiki abune da Gwamnati ke fahimta, kuma bazasu fasa shi ba.

Ihejirika yace “ASUU ba wani sabon abu take buƙata ba, a’a tana so duk abubuwan da aka yi yarjejeniya dasu a zartar dasu.

Ihejirika yace maimakon Gwamnatin Tarayya ta zartar da Yarjejeniyar Fahimta ta Shekarar 2009 sai ta zaɓi ta sanya su a tsarin Albashi na IPPIS.

Yace tsarin biyan Albashi na IPPIS ya taɓa Albashin lakcarori, kuma ya sanya basu karɓi Albashin su ba, na watanni da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram