An Kama Wani Matashi Da Yunƙurin Yin Garkuwa Da Ƴar Shekara 3 Saboda Ya Samu Kuɗin Da Zai Yi Aure

Rundunar Ƴansandan Katsina ta kama matashi da ta ke zargi da yunƙurin garkuwa da ƴar shekara 3 da nufin ya samu kuɗin da zai yi aure.

Matashin mai suna Nasidi Iliyasu mai shekaru 22 ɗan asalin ƙaramar hukumar Kaita ta jahar Katsina ne.

Nasidi ya bayyana cewa da dai da farko yayi niyar ya saci yarinyar amma daga baya sai zuciyarshi ta faɗa mashi wannan abu da ya ke niyar yi ba abu ba ne mai kyau.

Ku kalli bidiyon matashin a nan ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram