Ƴan ta’adda Sun Cika Wandunansu Da Iska Yayin Da Ƴansanda Suka Daƙile Wani Hari Da Suka Yi Yunƙurin Kaiwa A Katsina

Ƴan ta’adda sun ranta a nakare kuma sun bar baburan da suke aiki da su bayan da jami’an ƴan sanda suka daƙile harin da suka kai a ƙauyen Nassarawa dake maƙwabtaka ƙauyen Bugaje wanda ƙarƙashin ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina.

Kafar sadarwar Kakaki Network ta ruwaito cewa, daƙile harin ya biyo bayan samun bayanan sirri da rundunar ƴan sandan jihar tayi a jiya juma’a da ke nuna cewa wasu ƴan ta’adda da yawa a bisa babura sun farma ƙauyen Nassarawa da misalin ƙarfe huɗu na dare suna harbe harben bindiga ƙirar AK 47 a inda suka sace dabbobi da dama.

A wata sanarwa da Kakakin Rundunar SP Gambo Isah ya fitar a jiya da dare ta nuna cewa shugaban sashen rundunar da ya samu ƙwarewa kan daƙile ayyukan garkuwa da mutane ya jagoranci yan sanda zuwa wurin a inda suka fafata da ɓarayin dajin suka tsere kuma suka bar baburan su 2 da shanu 200, da tumaki 150 da kuma kayan saidawa na shago.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram