Rundunar ƴansanda a jahar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kama wani yaro mai ƙarncin shekaru da zargin satar ɗiyar kawunsa ƴar shekara 4 a duniya
Kakakin rundunar ƴansandan SP Gambo Isah ne ya gabatar da yaron mai suna Abubakar Abdulbasir ga manema labarai a jiya Juma’a a hedikwatarsu da ke Katsina
Ku kalli bidiyon yaron a nan ƙasa
A yayin zantawa da yaron ya ce ya saci yarinyar ne saboda yana son ya samu dubu 10 ya biya bashin kuɗin wata hula da ya saya.