Gwamnan jahar Katsina Amimu Masari zai bada kyautar Ƙatuwar mota ƙirar jeep ga babban zakara da kuma milyan 38 ga matasa 12 da suka zama zakaru a gasar ƙiƙira ta Katsina National Hunt Talent.
Kwamishinan Ma’aikatar yaɗa labaru na jahar Abdulkarim Yahaya Sirika ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Lahadin nan, a ɗakin taro na ma’aikatar da ke sakatariyar Katsina.
Ku kalli cikakken bayanin a cikin hoton bidiyon nan da ke ƙasa.
Taron bada kyaututtukan wanda za a yi a ranar Talata 15 ga watan Fabrairu na shekarar 2022, Sirika ya kuma ce bayan kyautar bilyan 5 ga kowane zakara a sashe da milyan 3 ga mai bi masa da kuma kyautar milyan 1.5 ga wanda ya yi da uku a kowanne fanni.