Mutumin nan mai suna Abdulmalik Tanko ya musanta zargin da ake masa na kisan da kuma garkuwa Hanifa Abubakar ƴar shekara 5.
A ranar Litin ɗin nan ne aka sake kai Tanko da mutane biyun da ake zargin sun aiakata laifin tare, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin a gaban Babbar Kotun jahar Kano ƙarƙashin jagorancin Alƙali Usman Na-Abba.
Da farko dai an karanto masu tuhume-tuhumen da ake yi masu, saidai dukkansu sun musanta.
Da aka tambayi Tanko yayi garkuwa da kuma kashe Hanifa? Sai ya ce, “ban aikataba.”