Ni Dama Can Ba Ɗan Kannywood Ba Ne Mutane Ne Ke Mana Kuɗin Goro -Naziru Sarkin Waƙa

Naziru sarkin waƙa ya ce shi dama tun asali ba ɗan kannywood ba ne kawai dai mutane ne ke masu kuɗin goro.

Naziru ya bayyana haka ne a cikin wani hoton bidiyo da ya saki a shafin sada zumunta inda ya ke bada haƙuri game da cecekucen da maganarsa da yayi akan Ladin Cima ta jawo.

Ya ce yan kannywood au yi haƙuri da abinda ya faɗa, ya ce shi haka ya ke in dai gaskiya ta zo to bai san lokacin da ya ke faɗarta ba.

Sarkin waƙar ya ce shi dama can ba ɗan kannywood ba ne kawai dai mutane ne ke masu kuɗin goro kuma suke ɗauka.

Daga karshe kuma ya bayyana bada kyautar naira milyan 2 ga ita Ladin Cima don ta fara sana’a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram