Dakataccen Ɗan sandan nan Abba Kyari ya ɗora alhakin sa ga Mambobin Ƙungiyar Tsagerun Biafra, da Jami’an tsaro na ESN, a matsayin waɗanda suke bayan abubuwan da suke faruwa, sakamakon yaƙar su da yayi a yankin Kudu maso Gabas.
Kyari ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Joseph Egbunike Mataimakin Sufeto-Janar na Ƴan sanda a hedikwatar hukumar ba Ƙasa.
Wannan ɗora alhaki yana ƙunshe ne a cikin wani rahoto da aka miƙa wa Sufeto-Janar na Ƴansanda Usman Baba, wanda daganan aka tura shi ga Hukumar Kula da Harkokin Ƴan sanda.
A cewar rahoton, Kyari bai musanta karya dokar Kafafen Sadarwa na Zamani da Hukumar Ƴan sanda ta sanya, amma kwamitin ya barranta kanshi akan jami’in domin an taɓa gargaɗin sa akan wannan karya doka.
“Wannan wani gangami ne domin ɓata suna na wanda mambobin IPOB/ESN suka ɗauki nauyin yi, sakamakon hana su sakat da yayi a yankin Kudu maso Gabas, inji Abba Kyari.
Amma kwamitin Binciken, sun yi fatali da wannan ɗora alhaki, inda suka bada shawarar a rage masa muƙami daga DCP Zuwa ACP na ƴan Sanda.
Duk wani ƙoƙarin na jin tabakin Hukumar Kula da Ƴan sanda domin jin kota karɓi rahoto wanda aka kawo mata akan Abba Kyari ba’a samu dama ba.
Duk kiran da aka yiwa lambobin mai Magana da Yawun Hukumar Ikechukwu Ani bai ɗaga ba, bai kuma maido da amsa akan saƙon da aka tura mashi ba.
Haka zalika, muƙaddashin Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Najeriya Muyiwa Adejobi bai ɗaga waya ba, ko maido da amsa akan saƙon da aka tura mashi, akan yunƙurin kare Abba Kyari, da kuma mako biyu da Hukumar Kula da Harkokin Ƴan sanda ta basu.