Da ɗuminsa: Babban Limami Mai Shekaru 130 A Kudancin Kaduna Ya Rasu

Babban Limamin Masarautar Jama’a a Ƙaramar Hukumar Jema’a dake Jahar Kaduna, Alhaji Sheikh Adam Tahir ya rasu yana da shekaru 130, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sheikh Adam ya mutu a Kaduna a ranar Laraba da yamma ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.

Dayake tabbatar da rasuwar ga Wakilin Majiyar mu, Mataimakin Limamin na Masarautar Jama’a Alhaji Muhammad Kabir D. Kassim yace Marigayin wanda ya shafe shekaru da dama yana jagorantar sallar Juma’a a Masallacin Juma’a na Kafanchan.

A takardar ta’aziyya, Mai martaba Sarkin Jama’a na Kafanchan, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya bayyana rasuwar limamin a matsayin rashi Babba a Masarautar Jama’a da Al’ummar Kaduna ta Kudu.

Takardar ta’aziyyar wadda Sakataran Masarautar ya sanya wa Hannu Alhaji Yakubu Isa (Dokajen Jama’a) ya bayyana kaɗuwa akan rasuwa Babbar Limamin, kuma ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki a Masarautar.

Ya kuma yi addu’a ga Allah daya jiƙansa.

Ibrahim Adam Tahir, ɗaya daga cikin ɗiyan marigayin ya shaida cewa Mahaifin su ya haifi ƴaƴa 50, amma ya rayu da ɗiya 26, da jikoki 290, da tattaɓa kunne 200, kuma za’a binne sa a gobe Alhamis da safe a Kafanchan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram