Kotu Ta Yanke Hukuncin Bulala 7 Ga Ɗan Kasuwar Da Ya Saci Gishiri A Kaduna

Wata kotun majistare dake Kaduna ta yanke wa wani dan kasuwa mai suna Nasiru Ahmed dan shekara 25 hukuncin bulala bakwai bisa laifin satar buhunan gishiri biyar.

Ahmed wanda ke zaune a unguwar Tudun Wada da ke Kaduna, an tuhume shi da laifin fasa shago da kuma yin sata.

Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Emmanuel ya yankewa Ahmed hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa kuma ya nemi a yi masa sassauci.

Tun da farko, mai gabatar da kara, Mista Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa wani Malam Abdulmalik Lateef ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Kawo a ranar 7 ga watan Fabrairu.

Mista Leo ya ce wanda ake tuhumar ya kutsa kai cikin kantin sayar da kaya na mai shigar da karar da ke Kasuwar Kawo, Kaduna, inda ya sace buhunan gishiri biyar da buhunan Fulawa guda biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram