Mai ba gwamanan jahar Katsina shawara a fannin tsaro, Ibrahim Katsina ya ce in dai za a yi adalci a faɗi gaskiya to sama da watanni 6 da suka wuce ba a samu wani ƙwaƙƙwaran hari ba a Katsina.
Kalli cikakken bayanin a cikin wannan hoton bidiyon da ke ƙasa.
Ibrahim Katsina ya shaida haka ne a yayin da Jakadiya ta zanta da shi game da sha’anin tsaro a jahar a Ofishinsa.
Ya ce irin kyawawan matakan da gwamna Masari ya ɗauka game da matsalar tsaro ya sa aka ɗauki sama da watanni 6 ba tare an samu harin da ya wuce ɗaya ko biyu ba a jahar