Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Hanya Mai Tsawon Kilomita 1.05 Ga Jami’ar Abuja

Gwamnatin Tarayya ta miƙa hanya mai tsawon sama da kilomita da aka sabunta, akan kuɗi Naira miliyan 186 wanda Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta yiwa Jami’ar Abuja UniAbuja a ranar Alhamis.

Hanyar dai, Kamfanin Messrs UKJ Consultant Nigeria Ltf., yayi kwangilar, ta haɗa sassa da dama na Makarantar, da suka haɗa da Wurin Malamai, da Sashen Ayyuka da Ɗakunan Ɗalibai.

Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola ya miƙa hanyar, a bikin ƙaddamar da aikin da miƙa aikin, daya gudana a Jami’ar.

Mr Fashola yace da wannan aiki a matsayin wata gudunmawa a ɓangaren ilmi, Gwamnati ta samu nasarar daukar wani ɓangare na samar da hanyoyi a Manyan Makarantu 46 na Gwamnatin Tarayya, tare da miƙa su 29 a ƙarshen 2021.

“A yayinda yake gaskiyane cewa ayyuka da dama suna buƙatar ayisu a ɓangare da dama na rayuwa, ciki har da ilmi, Gwamnatin Buhari na bakin ƙoƙari domin ta kammala ayyuka.

“Muna da hanyoyi 17 da suke a shirye domin miƙa su, a yayin da a halin yanzu muna yin hanyoyi 30 a Jami’o’i a faɗin Ƙasar nan, inda zai kasance munyi hanyoyi 76.

Ministan yace wannan kawo ɗauki a Jami’ar ta Abuja, yana daga wani ƙudirin Gwamanati na samar da cigaba a ɓangaren ɗan Adam domin tallafawa ilmi.

Mr Fashola ya samu wakilcin Babban Mai Kula da Ayyuka na Ƙasa na Abuja Usman Yakubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram