2023: Sanwa-Olu ya roƙi Ƴan Majalisar Lagos da suyi aiki tuƙuri domin samun nasarar Tinubu

Gwamnan Jahar Lagos Babajide Sanwa-Olu a ranar Juma’a ya roƙi Ƴan Majalisar Lagos na Jaha dana Gwamnatin Tarayya da suyi aiki tuƙuru domin tabbatar da samun nasarar ƙudirin Shugaban Ƙasa na Chief Bola Tinubu.

Mr Sanwa-Olu ya bada wannan shawarar a Ikeja a lokacin taron ƴan Majalisa da Majalisar Zartaswa karo na 17 da taken “tattara ƴan ƙasa a matsayin jari a Babban zaɓen shekarar 2023”.

Yace Tinubu ya sadaukar da kanshi ga Al’ummar Lagos a lokacin da yake Gwamna, dana Najeriya baki ɗaya, kuma an samu nasara mai yawa.

“Wannan lokaci ne da zamu biya shi da goyon bayan mu. Shine wanda yafi kowa cancanta ya zama Shugaban Ƙasa. Ya san al’amarin dake faruwa a Ƙasar nan, kamar tafin hannun sa, kuma zai iya kawo gyara.

“Saboda Jagoran mu Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, lokaci ne dazai kai Lagos a matakin Najeriya. Lokaci ne yanzu da zamu yi aiki tuƙuru tare da tabbatar da cewa nasarar daya samu a Lagos an same ta a Najeriya baki ɗaya.

“Wannan ne ya sanya nake son dukkanin mu, munyi duk abinda zamu iya a siyasa da wanda ba siyasa ba, domin tabbatar da cewa zamu iya taimaka, kuma mun samar da Shugaban Ƙasa na Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnan ya yabawa ƴan Majalisar akan ƙoƙarin wajen nasarorin da Gwmanatin sa ta samu a shekaru biyu da rabi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram