Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Kansila Da Wasu Mutum 8 A Sokoto

Wasu ƴan bindiga sun kai farmaki kauyen ‘Yar Tsakuwa da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto, inda suka yi awon gaba da mutane tara, ciki har da kansilan yankin, Lawali Bello (wanda aka fi sani da LBY).

Mata biyu da diyar tsohon Kansilan yankin Alhaji Abdullahi Garba na daga cikin wadanda aka sace.

Wani mazaunin garin mai suna Nazifi Abdullahi ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, ‘yan bindigar sun zo ne da sanyin safiyar yau Asabar inda suka yi ta harbe harbe har karfe 2:50 na safe.

Rahotanni sun ce sun yi ta afkawa cikin gidaje da shaguna da suka hada da shagunan sayar da magunguna, inda suka yi awon gaba da mutane da kuma kayayyakin su.

A cewar Abdullahi, barayin sun sace babura da kayan abinci da magunguna iri-iri.

Ya ce sun yi garkuwa da mutane sama da 20 amma sun sake wasu yayin da suke komawa maboyar su.

“Amma mutane tara a halin yanzu suna tare da su, ciki har da Kansilolinmu mai kan karagar mulki, da mata da ‘yar tsohon Kansilolinmu.”

Ya bayyana cewa tsohon kansila ya bar kauyen ne saboda hare-haren da ake kai musu ba kakkautawa, inda ya kara da cewa matan da diyar sun je kauyen ne domin halartar bikin nadin jikan da aka haifa.

Abdullahi ya ce ‘yan bindigar sun harbe wani mutum guda tare da raunata shi, Amma an kaishi zuwa wani babban asibitin Talatan Mafara da ke jihar Zamfara domin samun kulawa da lafiyarsa.

Da aka tambaye ko ‘yan fashin sun tuntube su domin neman kudin fansa, ya ce a’a.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, bai amsa kiran wayar da wakilin Jaridar Daily Truat ya yi masa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram