Najeriya Ta Samu Ƙarin Mutane 39 Da Suka Kamu Da Covid-19 A Jahohi 3, Da Abuja

Najeriya ta samu ƙarin mutane 39 da suka kamu da cutar Covid-19 a Jahohi guda 3 da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Hukumar Kula da Manyan Cututtuka ta Ƙasa ta bayyana haka a cikin sanarwar da take fitar wa duk kullum a ranar Juma’a, 18 ga watan Fabrairu na Shekarar 2022.

A cewar rahoton Hukumar, adadin mutane da suka kamu ya nuna cewa Lagos nada mutane 25 da suka kamu da cutar Covid-19, sai Rivers da Mutane 6, a yayinda Delta da Babban Birnin Tarayya Abuja aka samu mutane huɗu huɗu a ko’ina.

Hukumar tace mutane 25 da aka samu a Lagos sune aka samu 14 a ranar 17 ga watan Janairu, inda mutane 11 aka same su a ranar 18 ga watan Janairu.

Bayanan da Hukumar ta samu, ya nuna cewa an sallami mutane 19 bayan sun warke daga cutar.

Haka zalika, mutum ɗaya ya mutu a dalilin cutar Korona data kama shi.

Da sabbin mutanen da aka samu, yanzu Najeriya nada mutane 254,221 aka samu sun kamu da cutar, inda mutane dubu 230,549 suka warke, sai mutane 3,142 suka mutu a dalilin cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram