Gwamnan Jahar Kano a ranar Juma’a ya jaddada ƙudirin sa na ganin an haɗa kai, domin samar da jam’iyya mai ƙarfi a Jahar.
Mr Ganduje ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga dandazon magoya bayan Jam’iyyar, jim kaɗan bayan ya dawo daga Abuja, inda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da Shuwagabancin Abdullahi Abbas a matsayin Shugaban Jam’iyyar.
“Abinda ya faru a tsakanin mambobin jami’iyyar, faɗa ne na cikin gida.
“Muna tabbatar maku da cewa ƙudirin mu na haɗin kai da samar da Jam’iyya mai ƙarfi har yanzu yana nan.
“Har yanzu APC ita keda ƙarfi a Jahar Kano, itace Jam’iyya data kowane Jam’iyya ƙarfi a Jahar Kano, kuma APC ɗaya ce, kuma abinda ya faru rikici ne na ƴaƴan Jam’iyya.
“Muna gayyatar waɗanda suka kaimu Kotu dasu zo mu haɗa kai, domin mu cigaba da samar da Jam’iyya mai ƙarfi.
“Ina tabbatar maku dacewa ƙofa a buɗe take, muna siyasa ne, muna Son zaman lafiya.
“Duk wani rikici da ake yi ya zo ƙarshe, domin Kotun Ɗaukaka ta tabbatar da Shuwagabancin Abdullahi Abbas,” inji shi.
Gwamnan yace zai zauna da dukkanin Shuwagabannin Jam’iyyar na Ƙananan Hukumomi 44 domin tattaunawa akan dabarun da zasu yi wajen taimakawa domin Inganta yanayin Shuwagabancin Jam’iyyar, yana mai cewa a shirye suke domin halartar zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar na Ƙasa.
A jawabin shi, Shugaban Jam’iyyar APC na Jahar Alhaji Abdullahi Abbas, ya bada tabbacin tafiya da dukkanin mambobin jami’iyyar, tare da barin ƙofa domin bada shawarwari.