Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) a ranar Juma’a tace wata gobara data tashi a sansanin Ƴan gudun Hijira na Kalari Muna Elbadawy, ta kashe mutum ɗaya, tare da jikkata mutane 17 a Maiduguri ta Jahar Borno.
Babban Mai Kula da Bayanai na Hukumar NEMA na yankin Arewa Maso Gabas Abdulkadir Ibrahim ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a ranar Juma’a.
Ibrahim yace kimanin wuraren zama 100 suka ƙone, a yayinda ɗaruruwan mutane dake sansanin suka sake gudun hijira a dalilin lamarin.
Yace gobarar wadda ta fara daga ta dafa Abinci a wani tanti na Sansanin Ƴan Gudun Hijirar da misalin ƙarfe 1 na rana, Jami’an Kashe Gobara na Jahar sun samu nasarar shawo kanta.
Ibrahim ya bayyana cewar waɗanda suka samu raunukan an basu taimakon gaggawa.
Ya ƙara dacewa, Haɗakae Ma’aikata dana Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Kasa data Jaha sun je wurin domin gano adadin barnar da mutar da tayi a Sansanin.