Ƴan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wani Yaro Mai Taɓin Hankali A Bauchi

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar wani yaro dan shekara 14 da haihuwa a hanyar Dadin Kowa da ke karamar hukumar Ningi a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar,SP Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu ta wayar tarho a daren ranar Asabar.

Ya ce lamarin wanda ya faru a ranar Juma’a, mahaifin wanda lamarin ya shafa mai suna Haruna Shuaibu mai shekaru 38 ne ya kai rahoto a hedikwatar ‘yan sandan Ninigi.

Wakil ya ce mahaifin ya shaida wa ‘yan sanda cewa dansa mai suna Sadisu na da matsalar tabin hankali.

Ya ce, “Muna da shari’ar Mutuwar Kwatsam kuma wadda ba ta dace ba. A ranar 18 ga watan Fabrairun 2022 da misalin karfe 12:00 wani Haruna Shuaibu, dan shekara 38 a Titin Dadin Kowa, Ningi, ya kawo rahoto a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ningi cewa dansa mai suna Sadisu Haruna mai shekaru 14 ya rataye kansa dakin da ba a kammala ba a gidan

“Nan da nan da ‘yan sanda suka samu wannan bayanin, sai tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO suka je wurin da lamarin ya faru, suka garzaya da shi babban asibitin Ningi, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.

“Bayanan da aka samu daga mahaifin wanda lamarin ya shafa sun nuna cewa marigayin yana da tabin hankali.

“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Umar Sanda, ya umarci DPO Ningi, da ya fara bincike cikin gaggawa domin gano musabbabin mutuwar wanda iftila’in ya shafa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram