2023: Durojaiye Ya Bayyana Aniyarsa Na Tsayawa Takaran Shugabancin Kasa

Wani masani kuma ma’aikacin jinya a Najeriya da Amurka ta horar da shi, Dr Abdulfattah Durojaiye, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shelarar 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP).

Dan shekaru 53 daga jihar Ogun ya bayyana aniyar sa ne a ranar Asabar a Abuja babban Birnin Tarayya.

Ya kuma ce Buhari ba shi da wani dalili na kin rattaba hannu kan dokar gyaran zabe don tabbatar da cewa mutane irinsa za su iya tsayawa takara a cikin koshin lafiya.

Ya ce ya yanke shawarar tsayawa takara ne sakamakon yadda gwamnatocin da suka shude suka yi kasa a gwiwa, kuma kasar ta samu rarrabuwar kawuna a ‘yan kwanakin nan fiye da yadda aka samu a lokacin yakin basasa.

Kazalika ya Kara da cewa, ya zabi jam’iyyar PRP ne saboda akidar wadanda suka kafa jam’iyar da suka hada da Malam Aminu Kano da Alhaji Balarabe Musa, kuma shirin da zai yi wa Najeriya zai shafi harkokin ilimi, lafiya, tsaro da sauran sauye-sauyen tattalin arzikin zamantakewa da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram