Gwamnan Imo Ya Rarraba Wayoyin Hannu 2,700, Da Motoci Ga Matasa A Jahar

Gwamnan Jahar Imo Hope Uzodimma ya rarraba Wayoyin hannu 2,700 da Motoci guda 2 ga Matasa a matsayin wani aikace-aikace na murnar zagayowar ranar Masoya ta Duniya.

Uzodimma wanda ya rarraba kyaututtukan a wani taro da aka shirya a Owerri a ranar Asabar, ya kuma yi alkawarin samar da katin kira da shiga yanar gizo kyauta a garesu.

Sabbin motoci guda biyu an miƙa su ga wasu matasa guda biyu da suka samu nasarar lashe gasar da aka shirya anan take a wurin taron.

Gwamnan ya jaddada ƙudirin sa na tallafawa matasa ta hanyar samar masu da ayyukan yi, sai yayi kira a gare su dasu taimaka wajen gano ƴan ta’adda, domin samun zaman lafiya a Jahar.

Ya kuma sha alwashin bada irin waɗannan kyautukan a shiyyoyi guda 3 na Jahar, domin baiwa matasa a yankunan.

“Matasan Imo da Al’ummar Imo zasu ga ayyukan cigaba nan da watanni 18,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram