Sojoji dake ƙarƙashin Operation Whirl Stroke, a Jahar Benue a ranar Lahadi sun ceto mutane takwas daga maɓoyar masu garkuwa da mutane.
Wanda aka sacen, ƴan Asalin garin Agasha a Ƙaramar Hukumar Guma ta Jahar Benue, sun gamu da masu garkuwa da mutanen a lokacin da suke aiki a gonakin su a Larabar data gabata.
Mai Magana da Yawun Gwmanan Jahar Nathaniel Ikyur ya bayyana cewar waɗanda aka sacen sun shafe kwanaki uku a hannun masu garkuwa dasu kafin a ceto su.
Ikyur ya bayyana cewar Maiba Gwamna Shawara akan tsaro Laftanar-Kanal mai ritaya wanda ya bayyana wa Gwamnan irin samun nasarar da aka samu wajen ceto su, ya yaba da irin jajircewar jami’an sojin.
Yace sojojin sun gamu da masu garkuwa da mutanen a ƙauyen Gbekyor wanda ya haddasa musayar wuta, inda suka fi ƙarfin su, wanda ya sanya suka ruga Suka bar wanda aka ceton.
Ya ƙara dacewa waɗanda aka ceton an haɗa su da iyalan su.