Rashin Birki Ne Ke Haddasa Hatsari Kan Hanyar Owerri Zuwa Onitsha Ba Jami’anmu Ba – Inji Ƴan Sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, a ranar Asabar din da ta gabata, ta mayar da martani kan mummunan hatsari, wanda ya afku a wani shingen binciken ababen hawa da ke kan titin Onitsha zuwa Owerri, cikin karamar hukumar Ihiala ta jihar, inda ta ce ba mutanenta ne suka haddasa hatsarin ba.

Hatsarin wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu, ya faru ne a lokacin da wata babbar mota mai lamba UWZ 556 XA ta kutsa cikin wasu motoci shida a shingen binciken a ranar Juma’a.inda Wasu mutane tara suka samu raunuka a cikin wannan lamari.

An tattaro cewa direban babbar motar da ke kan babbar mota a lokacin da ya tunkari shingen binciken jami’an ‘yan sanda da ke unguwar Azia da ke Ihiala, inda ya rasa ikon sarrafa motar,ya yin daya kutsa cikin motocin da ke cikin jerin gwano.

A kalla mutane 63 ne hatsarin ya rutsa dasu yayin da wasu daga cikin motocin bas din fasinjoji ne.

An tattaro cewa an yi tashe-tashen hankula a wurin yayin da mambobin kungiyar direbobin manyan motoci suka tare babbar hanyar da suka lura cewa hatsarin ya afku a wani shingen bincike na ‘yan sanda a yankin.

Direbobin sun hada manyan motocin dakon kaya zuwa wurin da lamarin ya faru inda suka tare ko wane bangare na babbar hanyar, lamarin da ya haifar da kulle hanyar baki daya.

Direbobin manyan motocin ba su bayyana dalilin da ya sa suka dauki matakin ba, sai dai wani ganau ya ce suna zanga-zangar nuna rashin amincewa da barnar da shingen binciken ‘yan sanda ke yi kan masu ababen hawa a kan titin, domin an samu afkuwar irin wannan hatsarin a watannin baya a yankin.

Wani shaidan gani da ido ya koka da yadda a koda yaushe ana tambayar fasinjojin da su sauka daga cikin ababan hawa sannan sukan tilasata su wuce shingen binciken yayin da suke daga hannu biyu, matakin da ya zama nauyi ga jama’a.

Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar, Echeng Echeng, ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan, DCP Ikenga Tochukwu ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana direban motar a matsayin daya daga cikin wadanda suka mutu, ya kuma danganta hatsarin da wuce gona da iri da direban motar ya yi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an yi wa direbobin manyan motocin da ke zanga-zangar rashin fahimtar musabbabin hatsarin inda ta roke su da su sake tunani.

Sanarwar ta kara da cewa, “Duk da cewa ‘yan sanda suna da wurin bincike daf da wurin da hatsarin ya afku, amma ba daidai ba ne a zargi ‘yan sanda da aikata mummunan lamarin.

“Kasancewar motoci shida ne kawai ke cikin jerin gwano akan titin motoci biyu masu cike da cunkoson jama’a kasancewar wannan babbar hanyar hakan shaida ce da ke nuna cewa ‘yan sanda sun dau alhakin da kuma kula da halin da jama’a ke ciki ta hanyar tabbatar da bata lokaci kadan yayin da suke gudanar da ayyukan bincike da nufin kare ba wai kawai cibiyoyin ‘yan sanda a yankin daga hare-haren ‘yan tada kayar baya ba, har ma da sauran jama’a, wadanda akasarinsu ke fuskantar tserewa daga masu aikata laifuka.”

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta yabawa jami’anta da jami’an hukumar kiyaye haddura ta tarayya da suka tashi cikin gaggawa tare da yin hadin gwiwa da su wajen kai wadanda suka jikkata asibiti tare da kwashe baraguzan da ke kan hanyar domin a samu zirga-zirgar ababen hawa kyauta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram