Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth Ta Kamu Da Cutar Covid-19

Sarauniyar Ingila mai shekaru 95 ta kamu da cutar Covid-19 a ranar Lahadi, amma alamun da sauki, a yayin da ta buƙaci cigaba da ayyukan ta a gidan ta dake Windsor Castle, inji Mataimakin.

Labaran da suka shigo bayan Prince Charles, Babban Ɗan Sarauniyar, ya kamu da cutar a ranar 10 ga watan Fabrairu, kwana biyu bayan bayan ya ziyarci mahaifarsa a gidan ta na Windsor.

Babu wasu bayanai dake nuna cewa, Queen Elizabeth ta gudanar da awon da kanta.

“Fadarta ta Buckingham ta tabbatar da cewa Sarauniyar a ya an gwada ta, kuma an same ta da cutar Covid-19, inji sanarwar data fito daga Fadar ta.

“Sarauniya na fuskantar matsakaitan alamomi na cutar, amma zata cigaba da ayyukan ta a gida,” inji sanarwar.

“Zata cigaba da karɓar magani, kuma zata cigaba da bin dukkanin dokokin da aka gindaya akan cutar.”

Haka zalika, Fadar ta tabbatar da cewa an yima ta rigakafin da ake yi akan cutar Covid-19.

Saƙonnin fatan Alkhairi ga Sarauniya

Har yanzu babu wani jawabi daga bakin Firaministan Kasar Boris Johnson, Amma Sakataren shi Sajid Javid ya rubuta a shafin sa na Twita “ina yiwa Sarauniya fatan samun lafiya.”

Keir Starmer, Shugaban Jam’iyyar Hamayya shima ya rubuta a shafin sa na Twita “Ina yi maki fatan samun sauƙi, zaki samu lafiya mama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram